Tirkashi: Abin Ya Wuce Satar Kaya A Cikin Unguwanni Har Ya Kai Ga Ana Sata A Maƙabartu.

Spread the love

Jami’an Bijilante sun kama wani mutum mai suna Buhari da ake zargi da satar Allunan Maƙabartar Unguwa Uku dake karamar Hukumar Tarauni dake Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na dare ya yin da Jami’an Bijilante suke gudanar da aikin su, a gefan makabartar dake kusa da ofishin hukumar zabe INEC.

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa wanda ake zargi “ya ce sana’ar sa ita ce gwan-gwan, dan haka ya kan je makabarta dan sace allunan alamomi na kaburbura.

Rahotanni na nuni da cewa Al,umma na zargin ƴan gwan-gwan ne ke zuwa su kwashe allunan alamomi na kaburbura.

Sai dai wasu masu sana’ar ta tsince-tsincen kayan ƙarafan wato gwangwan a wannan yankin, sun musanta wannan zargi da ake yi musu.

Jihar Kano dai na da tarin maƙabartu da dama da babu hasken wutar lantarki, abin da wasu ke ganin cewa kan taimaka wajen bada mafaka ga masu zuwa su aikata miyagun laifuka a cikin su.

A wasu lokuta a baya, an sha samun waɗanda ke shiga maƙabartu a jihar da tsakar dare don tone gawarwaki, su ciri wasu sassan jikinsu dan wata mummunar manufa.

Adamu Abubakar Fiya Fiya Zonal Kwamandan Rundunar Bijilante dake Unguwa uku ya ce Rundunar ta samu nasarar cafke mutumin da ake zargin mai suna Bauhari .

Fiya Fiya ya ce bayan samun rahoton satar allunan maƙabarta a baya, ne ya sanya suka tsaurara Tsaron maƙabartar, kuma za su tura wanda ake zargin wajan jami’an ƴan sanda don fadada bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *