Trump ya ce ba zai sake yin wata muharawa da Kamala Harris ba

Spread the love

Ɗan takarar jam’iyyar Republican a zaɓen Amurka, Donald Trump ya ce ba zai sake yin muhawara ta biyu da Kamala Harris, ta jam’iyyar Demokrats ba gabanin zaɓen watan Nuwamban da ke tafe.

Tsohon shugaban Amurkan ya ce alƙaluma sun bayyana ƙarara cewa shi ne ya yi ”nasara” a muhawarar farko da ‘yan takarar biyu suka yi a birninPhiladelphia a farkon wannan makon.

Mista Trump ya ce ya kamata Kamala Harris ta ”mayar da hankali” kan aikinta na mataimakiyar shugaban Amurka.

A lokacin gangamin yaƙin neman zaɓenta a jihar North Carolina, Ms Haris ta ce masu kaɗa ƙuri’a na bin su bashin wata muhawarar.

Ƙuri’un jin ra’ayin jama’a sun nuna cewa ‘yan takarar biyu na kankankan yayin da ya rage ƙasa da wata biyu a gudanar da zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *