Tsananin Yunwa Da Wuya Ta Sanya Yaran Da Ake Zargi Da Zanga-zangar Yunwa Sun Suma A Kotu.

Spread the love

 

Ƙananan yara huɗu sun sume a kotu a lokacin da gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da su, kan zargin yunƙurin juyin mulki a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a watan Agusta.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da zaman na ta babu shiri bayan sumewar yaran a safiyar Juma’a.

Yaran ’yan ƙasa da shekaru 18 guda huɗu ne suka sume a cikin kotu a lokacin da aka gurfanar da su kan zargin su da yin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.

Sun Sume ne sakamakon tsanani da wuya, inda Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya dakatar da zaman kafin daga bisani a ci gaba da zaman bayan an fitar da su domin duba lafiyarsu.

Bidiyon yadda abin ya faru ya nuna yadda lauyoyi da ma’aikata suke ƙoƙarin taimakon yaran ’yan kasa da shekaru 18.

An kuma ga ana raba wa yaran biskit a cikin kotuna a yayin da lauyoyi ke kokawa bisa yadda aka bar wadanda ake zargin babu kula.

Yara 76 da aka tsare a jihohin Kano da Kaduna da Bauchi da sauransu ne aka gurfanar a gaban Babbar Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja kan zanga-zangar.

Idan ba a manta ba, Gwamnatin Tarayya ce ta gurfanar da waɗanda suka gudanar da zanga-zangar a watan Agusta, 2024 kan tuhumar su da laifuka 10, masu alaƙa da neman kifar da gwamnati.

Bayan karanta musu takardar tuhumar, matasan yaran sun musanta aikata laifin.

Daga nan alƙalin ya bayar da su beli a kan Naira miliyan 10 kowannensu.

Daga nan ya ba da umarnin tsare su a Gidajen Yarin Kuje har sai an cika sharuɗɗan belin.

Sharuddan sun haɗa da kawo wani babban ma’aikacin Gwamnatin Tarayya da ya mallaki lasisin tuƙi da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa ya tsaya musu.

Yarin Kuje har sai an cika sharuɗɗan belin.

Sharuddan sun haɗa da kawo wani babban ma’aikacin Gwamnatin Tarayya da ya mallaki lasisin tuƙi da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa ya tsaya musu.

Haka kuma za su kawo takardar shaida daga iyayensu ko kamu ’yan uwansu.

Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Janairun 2025.

Kungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam ta Amnesty International ta bukaci a yi adalci ga yaran waɗanda suka shafe watanni uku a tsare.

Ta bayyana takaici bisa tsarewar da aka yi musu saboda sun fito bayyana ra’ayinsu da kuma ’yancinsu a cikin ƙasarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *