Tsananin zafi ya tilasta rufe makarantu ga yara miliyan 33 a Bangladesh

Spread the love

Matsanancin zafi ya tilasta wa yara miliyan 33 daina zuwa makaranta a Bangladesh inda yanayin ya kai maki 42 a ma’aunin salshiyos.

Makarantu za su ci gaba da zama a rufe har zuwa 27 ga watan Afrilu. Wannan ce shekara ta biyu a jere da hukumomi suka ɗauki irin wannan matakin saboda zafin.

Philippines da Indiya ma a baya sun ɗauki irin wannan matakin yayin da ake fama da yanayin zafi a nahiyar Asiya.

“Yara a Bangladesh na cikin ƙasashe mafiya talauci a duniya kuma rufe makarantu saboda matsanancin zafi ya kamata ya zama abin fargaba,” in ji Shumon Sengupta, daraktan ƙungiyar Save the Children.

Bangladesh ɗaya ce cikin ƙasashe mafiya rauni ta fuskar sauyin yanayi.

A cewar ƙungiyar da ke fafutuka kan sauyin yanayi ta ce tumbasar teku na iya ɗaiɗaita mutum miliyan 35 daga lardunan da ke kusa da teku – kimanin kashi ɗaya bisa huɗu na al’ummar duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *