Tsarin Firaminista Ne Ya Fi Dacewa Da Najeriya —Aminu Dantata

Spread the love

Shahararren dan kasuwan nan, Alhaji Aminu Dantata, ya ce tsarin shugabancin firaminista da wasu ’yan majalisa suke nema shi ne mafi alheri ga kasar nan.

Dantata, ya bayyana haka ne a lokacin da wasu ’yan majalisar wakilai karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda suka kai masa ziyarar neman shawara a gidansa da ke Kano a ranar Alhamis.

Aminu Dantata ya ce, “Na gode da wannan ziyara, kuma ina yi wa wannan gagarumin gangami addu’ar samun nasara.

Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro

Kaunar Murja Kunya ya ratsa cikin zuciya ta don haka ku Aura mun ita: Ustaz Assalafi

“Tsarin firaminista ne ya fi dacewa da kasar nan saboda babu kashe kudin gudanarwa kaman tsarin shugaban kasa da muke bi.

“Ina fata za ku samu goyon bayan abokan aikinku, kuma ina rokon Allah Ya ba ku basira, Ya kuma yi muku jagora wajen cimma wannan kyakkyawan manufa ta taimakon kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *