Kan ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin mulkin Najeriya ya rabu game da tsarin mulkin da ya fi dacewa da kasar mafi yawan al’umma a Afirka – sama da mutum miliyan 200.
Yayin da wasu ke da ra’ayin komawa tsarin mulkin firaminista – wanda Najeriyar ta fara yi a jamhuriya ta farko a 1960 – wasu na da ra’ayin ci gaba da tafiya kan salon mulkin shugaban ƙasa mai cikakken iko da ake amfani da shi a yanzu a ƙasar.
Muhawara kan wannan batu ta ɓullo ne yanzu bayan wasau ‘yan majalisar wakilan ƙasar sama da 60 sun gabatar da ƙudurin neman gyara tsarin mulkin ƙasar na 1999 kan ƙasar ta koma amfani da tsarin firaminista.
Daga cikin dalilan da ‘yan majalisar ke bayarwa akwai neman rage kuɗaɗen tafiyar da gwamnati.
Dangane da hakan ne ƙwararru da masana da sauran masu ruwa da tsaki ke bayyana ra’ayoyinsu kan da tsarin da suke gani ya fi dacewa da Najeriyar.
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara
Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilan Najeriyar daga 2015 zuwa 2019, yana da ra’ayin komawa tsarin na firaminista, domin a cewarsa ta hakan za a daina yi wa kallon ‘yan majalisa abin da ake kira ‘yan-amshin-Shata.
Dogara ya ce tun da farko shi daman ra’ayinsa shi ne na tsarin mulki na firaminista, saboda a ƙarƙashin tsarin da ake mulkin Najeriya a yanzu na shugaba mai cikakken iko, shugaban ba shi da wata fargaba kan abin da zai biyo baya idan ya yi abin da bai dace ba.
”Mutumin da ke shugabanci wanda ba ya da tsoro ba ya abin da zai kawo mashi fargaba na cewar idan na yi kuskure akwai abin da fa za a iya min ko alabasshi an tsige shi daga mulki ko an ba shi wani horo to fa ba wani abin da zai sa shi ya yi wani abu na gari,” in ji Dogara.
Dangane da yadda wasu ke zargin ‘yan majalisar dokoki kama daga na jihohi zuwa na tarayya da sakaci abubuwa suka lalace har akan yi wa wasu da laƙabi da ‘yan-amshin-Shata, Dogara ya ce, masu wannan magana suna yi ne domin ba su san yanda tsarin mulkin ƙasar yake ba ne.
Ya ce ba wani abu da za ka iya yi don ka kawo barazana ga wanda ke Shugaban ƙasar Najeriya, saboda shugaban ƙasar ya sani babban lauyan gwamnati ya sani ba ta yadda za ka iya bin tanadin da kundin tsarin mulki ya yi na tsige shugaban ƙasa ka cimma wannan buri.
”Duk wani maganar da ake yi a Najeriya wai za a tsige shugaban ƙasa zancen banza ne kawai to ka ga duk irin illar da muke magana kenan,” in ji shi.
Tsohon shugaban majalisar wakilan ya ce dole ne ‘yan majalisa ya zama ɗan-amshin-Shata a tsarin da ake amfani da shi na shugaba mai cikakken iko a Najeriya.
Ya ce idan ba ka yi haka ba kana son muƙami ba za a ba ka ba, za a yi kaso ba kai, saboda haka dole ne ka bi ra’ayin shugabancidomin ta haka ne za a riƙa damawa da kai, ta yadda za ka samu hanyoyin yi wa jama’arka aiki.
Dogara ya ƙara da cewa, muddin dai ba a samu majalisar da za ta iya zama ta ce abin da shugaban ƙasa ya yi a’a ba mu yarda, kuma ya kamata mu tuhume shi, to ba ta yadda za a samu cigaba a Najeriya.
Tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau
sohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekaru, yana ganin har yanzu babu wani abu mai gamsarwa da ya ji daga masu sukar tsarin mulkin shugaba mai cikakken iko da ake amfani da shi a Najeriya, da ya kamata a bar shi a koma kan na firaminista.
Hasali ma ya ce tsarin mulkin firaminstan wanda Najeriya ta yi a jamhuriya ta farko , shi ne ma ya haifar da rigingimu da kashe-kashe da suka janyo har sojoji suka fara juyin mulki a Najeriya.
To amma tsohon sanatan ya ce -, su abin da suke magana a kai shi ne ba magana ce ta wane tsari za a yi ba, magana ce ta su waye za su gudanar da tsarin.
Sanata Shekarau ya ce duk kyawun tsari a rubuce idan aba a samu mutane masu nagarta da masu adalci da sanin ya kamata su jagoranci tsarin ba to ɓata lokaci ake yi kawai.
”Mu a wannan dandamali namu na League of Northern Democrats, ana cewa a koma tsarin faliyament (parliament) ba mu da ja to amma su waye za su yi jagorancin wannan tsarin su ne dai yanzu wanda suke siyasar nan,” in ji Shekarau.
‘Yanmajalisar Wakilai
Abdussamad Dasuƙi na daga cikin ‘yan majalisar wakilai sama da 60 da suka gabatar da ƙudurin sauya tsarin mulkin na Najeriya ta yadda za a koma tsarin firaminista, ya sheda wa BBC cewa a cikin shekara biyar ko shida na mulkin su Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto an ga irin cigaban da suka samar a ɗan taƙaitaccen lokacin da suka yi, saɓanin abin da ake gani yanzu a cewarsa.
Ya ce a ƙarƙashin tsarin da ake bi a yanzu sau da dama za su kawo abu a majalisa amma a ƙi yi, saboda haka wadannan na daga cikin abubuwa da suke ƙorafi a kansu a tsarin da ake mulkin Najeriya na shugaba mai cikakken iko da shi a yanzu.
Hon Dasuƙi, wanda ya ce za su ci gaba da wannan fafutuka ta neman mayar da ƙasar tsarin mulkin firaministan, ya ce sun bayar da dama ga duk wani ɗan Najeriya ya gabatar musu da shawara kan tsarin da yake ganin ya fi dacewa da ƙasar.
Farfesa Ango Abdullahi
Farfesa Ango Abdullahi wanda shi ne shugaban ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya Northern Elders Forum, ya ce komawa tsarin firaminista zai taimaka wa Najeriya wajen rage ɓarnatar da dukiyar ƙasa, da rage raɗaɗin halin da ƴan ƙasar ke fama da shi.
Ya ce tsarin shugaban ƙasa mai cikakken iko da ake amfani da shi a yanzu tsawon shekara 24, ya kasa ba wa Najeriya abin da tsarin firaminista ya bayar a cikin shekara biyar.
Ya ce idan ana maganar samun cigaba ne a yanzu, ai cigaban bai wuce na talauci da matsalar tsaro da sace-sace da sauransu, ”shi ne cigaban da aka samu,?” in ji shi.
Najeriya ta gudanar da mulki salon na firaminista a jamhuriyarta ta farko a ƙarƙashin kundin tsarin mulkinta na 1960 da kuma na 1963.
Daga 1960 zuwa 1963, shugaban ƙasar Najeriya a ƙarƙashin kundin tsarin mulki na 1960, ita ce Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II.
To amma kuma Dr Nnamdi Azikiwe ya kasance shugaban ƙasa na farko daga ranar 1 ga watan Oktoba, 1963 zuwa 16 ga watan Janairu 1966, yayin da Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa ya kasance Firaminista daga 1960 zuwa 1966, lokacin da sojoji suka yi juyin mulki na farko.