Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro Da Manyan Hafsoshin Tsaro Da Gwamnonin Arewacin Najeriya Sun Gana Akan Satar Mutane

Spread the love

Sakamakon yawaitar matsalar satar mutane a Najeriya, gwamnonin arewacin kasar sun amince da yin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da kuma duba yiyuwar yin amfani da wasu hanyoyin na daban wajen shawo kan karuwar matsalar tabarbarewar tsaro da take addabar yankin arewa.

 An cimma wadannan shawarwari ne a yayin wani taro da mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya kira tsakaninsa da kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya da manyan hafsoshin tsaro ciki harda Babban Sufeton ‘Yan Sanda da kuma kwamandan Rundunar Tsaron Sibil Difens.

An shafe fiye da sa’o’i 4 ana gudanar da taron wanda ya gudana cikin sirri sa’annan bayan kammala shi Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe yayi karin haske game da abubuwan da aka tattauna akai.

Ya kuma bayyana shirin kungiyar gwamnonin ta yin amfani da wasu hanyoyi na daban wajen shawo kan tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya.

Kankarar Da Ake Sayarwa Kan Naira 100 Guda Daya Kafin Zuwan Watan Azumi, Yanzu Duk Guda Daya Ta Koma Naira 700 A Kano.

A daina zancen kabilanci da kalaman kiyayya – Miyatti Allah- (MACBAN)

Gwamnan ya kara da cewar za’a nemi gudunmowar sojoji wajen murkushe masu tada kayar baya ba tare da yin amfani da karfi ba.

“Kamar yadda kuke gani, wannan taro ne tsakanin gwamnonin arewacin Najeriya da manyan hafsoshin tsaro da kuma mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro”.

Ya cigaba da cewar, “wannan taro ne daya shafi tsaro, kuma kun san irin mahimmancin da tsaro keda shi, musammamma yanzu da matsalar yin garkuwa da mutane ke kara karuwa a shiyar arewa maso yamma, don haka akwai bukatar mu tattauna mu sake nazari tare da rungumar wasu dabarun na daban akan wadanda muke yi domin samun mafita”.

A makon daya gabata ne , ‘yan bindiga suka sace kusan dalibai 300 daga wata makaranta a kauyen kuriga dake karamar hukumar chikun ta jihar kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *