Alkaluman tsawon rai a tsakanin ‘yan Najeriya maza da mata sannu a hankali sun karu tun daga shekara ta 2015 zuwa 2022, a cewar hukumar kididdiga ta kasar.
Wannan na kunshe ne a cikin wani rahoton kididdiga na hukumar don shekara ta 2022 da aka fitar ranar Talata a Abuja.
Rahoton ya ce tsawon rai tun daga haihuwa ga ‘ya’ya maza a Najeriya ya karu daga shekara 53.2 a 2015 zuwa shekara 55.1 a 2022, yayin da tsawon ran mata a Najeriya ya karu daga shekara 55.3 a 2015 zuwa shekara 57.2 a 2022.
“Wannan karuwa na nuna cewa an samu ci gaba a tsawon wannan lokaci game da koshin lafiyar mata da kananan yara, kuma an samu bunkasar harkokin kula da lafiya,” cewar rahoton.
“Ya kuma nuna cewa an samu raguwar alkaluman mace-mace mai alaka da wani takamaiman sanadi.”
Hukumar kididdiga ta Najeriya ta kuma ce don samun karin ingancin tsawon rayuwa a Najeriya, akwai bukatar gwamnati ta zuba kudi a shirye-shirye da manufofin bunkasa lafiya masu matukar tasiri.