Tsoffin gwamnonin Zamfara huɗu sun gana kan ‘matsalar tsaron jihar’

Spread the love

Tsofaffin gwamnonin jihar Zamfara huɗu sun yi wata ganarwar sirri domin tattauna yadda za a magance matsalar tsaro da ke addabar jihar.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar ya ce tsofaffin gwamnonin jihar – da suka haɗa Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura da Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi da Sanata Abdulaziz Yari Abubakar da kuma ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Bello Mohammed Matawalle – sun gana ne a jiya da Asabar da daddare.

”Tsoffin gwamnonin – da suka gana a gidan ministan tsaron – sun ɗauki tsawon lokaci suna tattaunawa kan batutuwan da suka shafi matsalar tsaron jihar da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar, don inganta ci gaban rayuwar al’ummar jihar ta fannonin ilimi da na lafiya”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ambato gwamnonin na cewa idan ana batun tsaro, ya kamata a ajiye duk wani bambanci musamman na siyasa da ke tsakani domin sama wa al’umma mafita.

A baya-bayan nan dai jihar Zamfara na fama da ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga da ke sace mutane domin neman kudin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *