Tsohon shugaban hukumar NYSC ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga

Spread the love

Tsohon shugaban NYSC ya kuɓuta daga masu garkuwa da mutane

Tsohon shugaban NYSC, Maharazu Tsiga ya kuɓuta daga hannun ƴanbindiga da suka yi garkuwa da shi.

Kafar Channels ce ta ruwaito hakan, inda ta ce tsohon janar ɗin ya kuɓuta ne a ranar Juma’a bayan ya shafe kwana 22 a hannunsu.

Da farko dai ƴanbindigar sun buƙaci naira miliyan 250 ne a matsayin kuɗin fansa kafin su sake shi.

Sai dai babu tabbacin yadda ta kaya kan batun kuɗin fansar har zuwa lokacin haɗa wannan labarin.

An yi garkuwa da tsohon hafsan sojan ne a ranar 6 ga Fabrairun bana a gidansa da ke Tsiga a ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar Katsina.

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Fitar Da Sabbin Matakan Tsaro A Watan Azumin Ramadana

A gaban mijina Akpabio ya nemi kwanciya da ni —Sanata Natasha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *