Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar ƙasar su koma gona don noma abin da za a ci domin magance matsalar tsadar abinci a ƙasar.
Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar wa manema labarai jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi a birnin Daura da ke jihar Katsina.
“Ina amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan Najeriya su zama masu dogaro da kai. Mu koma gona domin noma abin da za mu ci,alamu sun nuna cewa za mu iya, wannan ba lokacin zama ba ne, duba da yadda farashin abinci ke tashin gauron zabbi”, in ji Buhari.
“Mu riƙa sayen abubuwan da ake samarwa a ƙasarmu, gwamnatocin ƙasarmu sun yi shirye-shirye masu yawa na ci gaban ƙasarmu, kuma ina ƙarfafa wa mutane gwiwa, musamman matasa su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasarmu”, in ji tsohon shugaban ƙasar.