Tsohon shugaban Saliyo zai tafi Najeriya don neman lafiya

Spread the love

Tsohon shugaban Saliyo zai tafi Najeriya domin neman lafiya, duk kuwa da shari’ar da yake fuskanta a ƙasar bisa zargin hannu a yunƙurin juyin mulkin ƙasar cikin shekarar da ta gabata.

A ranar Laraba ne babbar kotun ƙasar ta bai wa Ernest Bai Koroma damar ficewa daga ƙasar na aƙalla wata uku.

To sai dai ana ganin cewa an cimma yarjejeniyar barinsa ya je zaman gudun hijira.

A watan Maris ake sa ran fara shari’ar da ake yi masa kan zargin cin amanar ƙasa.

Mista Koroma ya kwashe shekara 11 yana jagorantar Saliyo, har zuwa shekarar 2018 lokacin da aka zaɓi shugaba Julius Maada Bio a matsayin sabon shugaban ƙasar.

An ga jirgin saman shugaban Najeriya ɗauke da Mista Koroma, lokacin da yake barin filin jirgin saman birnin Freetown ranar Juma’a da rana.

Matakin na zuwa ne bayan da aka yi ta samun rahotonnin da ke cewa ƙungiyar Ecowas ta shiga tsakani domin cimma matsaya da gwamnatin Saliyo wanda ya bai wa tsohon shugaban ƙasar mai shekara 70 damar ficewa daga ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *