Wani lauya dan gwargwarmaya da ke fafutukar tabbatar da adalci a jahar Kano, Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya shigar da korafinsa ga hukumar tsaron farin kaya ta kasa DSS, kan kalaman tunzuri da batanci da DR. Idris Dutsen Tanshi da kuma Sheik Baffa Hotoro, suka yi ga al’ummar garin Tudun Biri a karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna.
Cikin takaddar korafin mai shafuka uku, da idongari.ng ya gani, wadda Barista Badamasi Gandu, ya ce masu gabatar da Maulidin a garin Tudun Biri , iftila’in Bomb ya fada mu su yayin da wasu suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata sakamakon iftila’in.
Sai dai lauyan ya bayyana mamakin sa na yadda wasu malamai dake son tada ricikin addani da kuma kalaman tunzuri da suka furta ga mutanen da iftala’in ya fada wa abunda damuwa ne da zama wajibi a dauki mataki a kansu dan gudun kaucewa matsala anan gaba.
Ya kara da cewa hatta gwamnatin tarayya ta yi Allah wadai da abunda ya faru ga al’ummar Tudun Biri harta alkawarta biyan diya, ga iyalan wadanda harin ya shafa, dadin dada wa shima sarkin Musilmi da tsohon sarkin Kano Alhaji Mahammadu Sunusi na ii , duk sun yi Allah wadai da hakan tare da kwantarwa da al’umma hankali.
Barista Gandu ya ce abun mamakin da takaici na yadda wasu malamai maimakon su yi shiru da bakin su tunda ba za su yi addu’a ba ko yin jajen abinda ya faru , sai kawai suka dinga aike wa da kalaman tunzuri ga al’ummar Garin Tudun Biri.
Cikin wasu kalaman malaman na cewa” Duk wanda ya mutu yayin da yake yin Maulidi to ya mutu ne yana aikata sabo , kuma ba zai samu rahmar ubangiji ba , gwarama mutum ya mutu yana aikata Luwadi ko zina” cewar Dutsen tanshi da Baffa Hotoro”.
Lauyan ya ce wadannan kalaman tunzuri ne , shi ya sa yayi korafin su ga hukumar tsaron farin kaya dan a gayyace su , a ladabtar da su dan samar da zaman lafiya a Nijriya kuma samun arziki mai dorewa.
A makon da ya gabata ne, akaga faifan bidiyon Malaman Malaman ya na yawo a shafukan sada zumunta inda suke furta kalaman batancin ga al’ummar garin Tudun Biri, wanda yin hakan zai iya tunzura al’umma .
A baya ma dai Dushen tashin da kuma Baffa Hotoro , an tuhume su da furta kalaman da za su iya haifar da riciki.