Uba Sani ya mayar wa iyalan Abacha filayen da El-Rufai ya ƙwace musu

Spread the love

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya mayar wa iyalan Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Sani Abacha, filayensu guda biyu da tsohon jihar, Nasir El-Rufai ya ƙwace a lokacin mulkinsa.

Lauyan iyalan Abacha, Reuben Atabo, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

A cewar sanarwar da Babban Daraktan Ma’aikatar Kula da Filaye ta Jihar Kaduna, Mustapha Haruna ya fitar, Gwamna Uba Sani ya aike wa iyalan Abacha wasiƙa.

A wasiƙar, an tabbatar da mayar musu da filayen sannan an buƙaci su biya harajin da aka saba karɓa sakamakon mallakar filayen.

Tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya ƙwace filayen ne a ranar 28 ga watan Afrilun 2022.

Bayan ƙwace filayen, ya sanar da matakin nasa a cikin jaridu tare da soke

Sai dai matakin na El-Rufai ya haifar da cece-kuce, inda wasu ke ganin tsohon gwamnan bai kyauta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *