Wani dan majalisar Amurka Scot Perry ya bayyana cewa hukumar raya kasashe ta kasar Amurka tana samar da kudi don ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda ciki hadda kungiyar boko Haram.
Mr. Perry wanda dan jam’iyyar Republican ne yayi wan nan zargi ne yayin wani zaman karamin kwamitin majalisar kan ayyukan hukumomin gwamnatin kasar ta Amurka.
Yace hukumar ta USAID ta amurka baya ga boko haram tana daukar nauyin kungiyoyin yan ta’adda kamar su ISIS da ALQAEDA.
Dan majalisar na amurka yace hukumar ta USAID itace take daukar nauyin bada horo ga sabbin shiga wadan nan kuniyoyi na ‘yan ta’adda.
Mr. Perry ya kuma bada misalin wasu kudade da suka kai dala miliyan 136 da hukumar ta USAID tace ta gina makarantu 126 a pakistan amman babu wata shaida data bayar na gina makarantun.
- Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano
- Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano