Waɗansu na son na yi wa Kwankwaso butulci – Abba

Spread the love

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna matukar damuwa kan wadanda ya kira masu son a samu tashin hankalin siyasa tsakaninsa da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwanso inda ya ce wadannan mutanen na son ya yi wa butulci ga shugabansa na tsawon lokaci.

A karon farko tun da aka soma yaɗa jita-jitar cewa akwai rashin fahimta a tsakanin shugabannin biyu, gwamnan Kano ya nuna ɓacin ransa a lokacin wata tattaunawa da ‘yan jarida, inda ya ce Kwankwaso jagora ne da bai kamata ƙananan ‘yan siyasa su dinga yi masa raini ba.

“Abin da ake nema a gare ni shi ne in yi butulci. Ma’anar ‘Abba tsaya da kafarka’ kenan. Abba tsaya da kafarka cin fuska ne a wajena. Tsakanina da Kwankwaso babu rigima,” in ji gwamna Abba Kabir Yusuf.

Gwamnan ya ƙara da cewa “ina mamaki! so ake in je in ci masa mutunci ? Kanawa ba a san mu da cin amana ba. So ake in ci mutuncin wanda yayi min sila ?

A cewar Abba Kabir Yusuf ba zai yi butulci ga wanda ya yi masa silar zama gwamna ba kuma ya karyata cewa Kwankwaso ya kira shi a wayar tarho amma bai dauka ba

“Shekaru na 40 ina tare da Kwankwaso ba a taba jin kanmu ba, sai lokacin da na zama gwamna za a nemi a jawo mana fitina. Ina tare da shi tsawon lokaci duk inda ya bi a siyasa tare muke tafiya,”in ji gwamnan.

Gwamnan na Kano ya ƙara da cewa babu rashin jituwa tsakaninsa da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

‘Abba tsaya da ƙafarka’

A cewar gwamna Abba Kabir Yusuf cin fuska ne gare shi masu cewa ‘ya tsaya da kafarsa’. Saboda a cewarsa mutane na sha’awar irin abubuwan da suke yi a jihar Kano kuma batun tsayawa da kafarka na da ma’ana da yawa.

“Ina kira indai mutum masoyina ne, ko a gwamnati ko a siyance ko a mu’amalance daga yau ka da gwamna ya ƙara jin maganar tsaya da kafarka. Kuma duk wanda ya yi ina son al’umma su yi masa hukunci ba da yawuna ba,” in ji Abba Gida Gida.

Waɗannan kalaman na gwamnan Kano za su yayyafa wa ƙurar rikicin da ake zargin ta kunno kai a jam’iyyar NNPP kuma bisa dukkan alamu hakan ya nuna cewa Abba Kabir Yusuf zai ci gaba da biyayya ga jagoran na jam’iyyarsu Rabiu Musa Kwankwaso.

A farkon wannan makon ne wadansu ‘yan majalisar wakilai suka nesanta kansu da tafiyar kwankwasiyya bisa zargin cewa jagoran jam’iyyar Rabiu Musa Kwankwaso na babakere a kan al’amura.

‘Yan majalisar tarayyar su ne Ali Sani Madakin Gini da kuma Kabiru Alhassan Rurum waɗanda suka sanar da ficewa daga tsarin kwankwasiyya, amma suna cikin jam’iyyar.

Tun a makonnin da suka wuce ne jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da sakataren gwamnatin Kano, Baff Bichi da kuma wani kwamishina Muhammad Diggol bisa zargin su da rashin biyayya ga jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *