Wa’adin biyan kudin aikin Hajjin bana a Najeriya ya cika

Spread the love

Da misalin karfe goma sha biyun daren ranar Jumma’a 31 ga watan Janairun 2025, ne wa’adin biyan kudin kujerun aikin hajjin bana ya kare, sai dai kuma har ya zuwa karewar wannan wa’adi, maniyyata aikin Hajjin Najeriya da dama ba su sami kammala biyan kudinsu a jihohin kasar ba, kuma suna ta kiraye-kirayen a kara lokaci.

Hajiya Fatima Sanda Usara, mataimakiyar daraktar sashen watsa labarai a hukumar aikin Hajji ta Najeriya, wato NAHCON, ta shaida wa BBC cewa, idan har akwai wani sabon bayani a game da kara wa’adin biyan kudin to hukumarsu za ta sanar.

Ta ce daga bayanan da suke samu daga jihohi kawo yanzu mutane sun biya kudinsu domin akwai ma wadanda suka biya kudin da ya zarta wanda aka sanar sakamakon hasashen cewa kudin kujerar bana zai iya kai wa Naira miliyan 10.

” Yanzu irin wadannan mutane da suka biya kudin daya zarta na kujerar suna ta murna bayan sanar da kudin kujerar ta bana, kuma nan bada jimawa ba za a mayar musu da sauran kudinsu bayan an cire wanda ya kamata.” In ji ta.

Hajiya Fatima Sanda Usara, ta ce,” Akwai kuma maniyyatan da ke bukatar a kara wa’adin biyan kudin kujerar wand su kuma sai jira bayanin da zai biyo baya daga hukumar nan bada jimawa.”

Rahotannin dai na cewa Ba lallai Najeriya ta cike kujerun da ƙasar Saudiya ta ware mata ba a hajjin bana sakamakon samun ƙarancin masu biyan kuɗi a yayin da wa’adin da aka sanya na biyan kuɗi ya cika.

A ranar 20 ga watan Janairun 2025, ne hukumar aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta sanar da sabon farashin kujerar aikin Hajjin bana.

A hirarsa da BBC, shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya ce kujerar aikin hajjin kamar yaushe ta kasu kashi uku inda wadanda za su je Hajjin daga kudancin Najeriya kudinsu ya fi na wadanda zasu tashi daga arewa maso gabas da kuma arewa maso yammancin Najeriya.

Ya ce “Ga alhazan da za su tashi daga jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya kamar Kano da Kaduna da Jigawa da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi, za su biya kudin da ya kai naira miliyan 8.45.

“Sai kuma wadanda za su tashi daga arewa maso gabashin Najeriya wadanda su sun fi kusa da Makka, wato wadanda suka fito daga jihohin Adamawa da Yobe da Borno da Gombe da Bauchi da kuma Taraba za su biya naira miliyan 8.32.”

“Wadanda za su tashi daga jihohin kudancin Najeriya kuma za su biya naira miliyan 8.78,” in ji shi.

Shugaban hukumar na NAHCON, ya ce kudin kujerar aikin hajjin ta bana da kadan ya dara na bara.

Ya ce “Da farko mun tsorata domin muna ganin kudin kujerar bana zai iya kai wa naira miliyan 10 koma fiye da haka, to amma da taimakon Allah da kuma tuntuba da bibiyar wadanda ke yi wa alhazai hidima a can Saudiya da muka yi shi ya sa aka samu sauki.”

BBCHAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *