Wacce ƙungiyar tsaro ce Miyetti-Allah ta kafa,kuma mene ne ayyukanta?

Spread the love

A baya bayan nan ne Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta kaddamar da wata kungiya ta ƴan sa-kai domin taimakawa wajen inganta tsaro ga mambobinta, musamman yankunan da aka fi fama da matsalar tsaro.

Ƙungiyar da aka yi wa lakabi da Nomadic Vigilante a Ingilishi ta tantance fiye da mutane 2,000 a jihar Nassarawa.

Shugaban kungiyar ta Miyetti Allah Kautal Hore na ƙasa, Bello Abdullahi Bodejo ya shaida wa BBC Hausa cewa an kafa kungiyar ce domin ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro a yakin da suke da ƴanbindiga da masu satar mutane don neman kuɗin fansa da sace-sacen dabbobi a jihar Nassarawa.

“Za su haɗa kai da jami’an tsaro – soja da ƴansanda da DSS a nemi wanda ake nema cikin lalama ba tare da an kashe wanda bai ji ba bai gani ba.” in ji Bodejo.

Bello Bodejo ya ce ba su kai ga samun amincewar gwamnati ba a kan wannan ƙudiri na kafa ƙungiyar ba, amma yana fatan cewa gwamnati za ta bayar da goyon baya.

“Muna fata ta samu amincewar gwamnatin tarayya ko kuma hukumomin tsaro saboda taimaka wa gwamnati za mu yi, kuma za mu taimaka wa gwamnonin Najeriya a kan abin da muka dauko.”

IGP ya bayar da naira biliyan biyu ga iyalan ‘yan sandan da suka mutu

A yanzu haka ƙungiyar na da jami’ai fiye da 2,000 waɗanda aka ƙaddamar a jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya.

Shugaban Miyetti-Allah na ƙasa, Bello Bodejo ya ce tun farko sun yi niyyar ƙaddamar da mutum 4,000 a kungiyar sai dai sun tantance kimanin mutum 2,140 a jihar Nassarawa.

A cewarsa, wannan ya nuna cewa “mun san ina ne gidajen suke kuma mun san da cewa watakila akwai wahala ya zama wanda muka sa ya kasance akwai dan ta’adda a gidansu ya bari.” in ji Bodejo.

Hukumar KAROTA ta musanta wani rubutu da ta gani yana yawo da sunan ta

Ya ce fatansu shi ne su samu fahimtar gwamnati da sauran hukumomin tsaro a kan manufarsu ta kafa kungiyar.

“Mun fara da jihar Nassarawa, ina fata nan da wata shida duk wani al’amari da yake faruwa a jihar Nassarawa ba za a sake jin sa ba, In sha Allahu.” in ji Shugaban na Miyetti Allah.

Manufar ƙungiyar

Shugaban kungiyar ta Miyetti Allah ya ce maƙasudin kafa kungiyar shi ne domin tabbatar da adalci wajen hukunta mutanen da aka samu da laifi.

Ya ce a lokuta da dama idan an kama mutum, ba a bincike sai a kashe shi.

Ya ce wannan dalili ne ya sa suka bai wa mutanen da ƙungiyar ta ɗauka horo ƙarƙashin jami’an tsaro da tsofaffin jami’an tsaro.

“Ba ma buƙatar a kashe mutum ko da ma ɓarawo ne.” kamar yadda ya ce.

A cewarsa, “za mu wayar wa yaran Fulani kai idan aka samu mai laifi, babu duka babu zagi a miƙa shi ga jami’an tsaro su yi bincike idan har aka tabbatar da laifin mutum a gabatar da shi a gaban kotu.”

Ya tsarin ayyukan kungiyar tsaron ta sa-kai?

Shugaban na Miyetti Allah Kautal Hore ya ce asali Fulani “an san shi da sanda” sai dai ya ce za su samar wa ƴan ƙungiyar makamai daidai da tanadin dokar ƙasa.

“Dole mu samar musu abin da duk doka ta yarda da shi cewa su rike za mu nema musu.” in ji Bodejo.

Matsalar tsaro da ke addabar makiyaya

A tsawon lokaci, Fulani makiyaya da manoma sun kasance suna zama na amana da taimakon juna, sai dai a gwamman shekaru da suka gabata lamarin ya rikiɗe zuwa kashe-kashen juna da gaba.

A yanzu labarin rikice-rikice tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma a Najeriya ya zamo jiki, inda kusan a kowane mako akan samu rahoton irin wannan matsala.

Hakan ya haifar da asarar rayuka da dukiya mai ɗimbin yawa, wadda sai dai a yi ƙiyasi kasancewar babu wanda zai iya faɗin takamaiman alƙaluma.

A shekarar 2016, wani rahoto na ƙungiyar bayar da tallafi ta Mercy Corps ya bayyana cewa rikicin manoma da makiyaya a Najeriya na haifar da asarar aƙalla dalar Amurka biliyan 14 a kowace shekara.

Wannan matsala ta fi ƙamari ne a yankin arewa maso tsakiyar Najeriya, musamman a jihohin Nasarawa da Benue da kuma Filato.

Ko da lamarin ya lafa, bayan wasu ƴan kwanaki sai matsalar ta sake rincaɓewa, ko ma ta ƙazance fiye da baya.

Wata babbar matsala da ke addabar al’ummar Fulanin a Najeriya ita ce ta masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Matsalar wadda ta ƙazance a arewacin Najeriya cikin ƙasa da shekara goma da ta wuce ta jefa makiyayan cikin halin gaba-kura-baya-sayaki.

Yawancin waɗanda ake zargi da hannu wajen aikata wannan laifi makiyayan ne, sai dai da dama daga cikinsu su ma sun sha wahala a hannun masu garkuwa da mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *