Waiya ya kaddamar da kungiyar masu tallata aiyukan gwamnan Kano a Facebook

Spread the love

 

 

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya kaddamar da kungiyar masu tallata aiyukan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a Facebook.

Yayin da yake kaddamar da su a yau lahadi, Waiya ya bayyana cewa gwamnan Kano yana aiyuka sosai don ciyar da jihar Kano gaba, amma kuma ba a yada aiyukan yadda ya kamata.

Ya bukaci ya’yan kungiyar da su yi amfani da shafukansa da kwarewar da suke da ita wajen tallata aiyukan alkhairin da gwamnan Kano yake yiwa kanawa.

” A wannan lokacin ya kamata ku sani Facebook ba wajen yin rawa da waka ba ne kadai, tun da kuna da mabiya to zaku iya amfani da shafukan naku wajen sanar da al’umma aiyukan gwamnan Kano ko kuma ilimantar da al’umma aiyukan gwamnan”. Inji Waiya

Kwamared Waiya ya baiwa ya’yan kungiyar tabbacin gwamnatin jihar Kano zata taimaka musu da kayan aiki sannan a basu horon yadda za su gudanar da aiyukan yadd

a ya Kamata.

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar Abdulrahman Hamisu ya baiwa kwamishinan tabbacin za su yi aiki tukuru don yada aiyuka da manufofin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *