Wakilin kananan hukumomin Rano, Kibiya, Bunkure a majalissar tarayya Hon. Kabiru Rurum, ya yi alhinin rasuwar Rt Ghali Umar Na’abba

Spread the love

 

Maigirma Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Kuma wakilin kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a Majalisar wakilai ta kasa na Mika sakon ta’aziyyar rashin Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Rt Hon Ghali Umar Na’abba* Wanda Allah yayiwa rasuwa tsakar daren larabar nan.

Babu Shakka Rt Hon Ghali Umar Na’abba shugaba ne daya rayu cikin hidimtawa Al’umma da kokari wajen ganin an kyautata rayuwar masu karamin karfi..

A madadin daukacin Al’ummar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure da dukkanin ‘Yan gidan siyasarsa, Rt Hon Rurum na Addu’ar Allah ya jikan marigayin ya gafarta masa yasa Jannatul Firdausi ta zam Makoma gareshi Amin…

*Fatihu Yusuf Bichi*
*Media Aide (Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *