A wannan makon ne gamnatin Najeriya ta ce ba za ta biya ko sisin kwabo ga ‘yan bindigar da suka sace daliban makarantar Kuriga domin su saki daliban ba.
A makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka yi wa makarantar Kuriga kawanya tare da sace daliban kusan 300.
Kusan mako guda bayan sace daliban ne ‘yan bindigar suka kira wani daga cikin iyayen daliban, inda suka bukaci a biya su kimanin naira biliyan daya domin su saki daliban.
‘Yan bindigar sun yi wa iyayen barazanar kashe daliban idan ba a biya su kudin fansar da suka bukata ba.
A nasu bangare iyayen yara sun koka kan halin matsin da suke ciki, inda suka ce ba sa iya samun abinci sau uku a rana, ina za su samu wadannan kudi da ‘yan bindigar suka bukata.
To sai dai gwamnatin kasar ta ce ba za ta biya kudi don sakin daliban ba, a cikin wani jawabi da ministan yada labaran kasar Mohammed Idris ya yi wa manema labarai jim kadan bayan taron majalisar zartarwar kasar ranar Laraba, ya ce gwamnatin kasar za ta yi duk abin da ya dace domin kubutar da daliban.
Mohammed Idris ya ce idan ta kama gwamnati za ta yi amfani da karfi don ceto daliban.
Shin ya dace gwamnati ta biya kudin fansa?
Barista Audu Bulama Bukarti, mai sharhi kan al’amuran tsaro ya ce ya goyi bayan matakin gwanatin Najeriya na kin biyan kudin fansa ga ‘yan bingida.
Masanin ya ce ”duk da na san cewa iyayen yara yanzu suna cikin halin damuwa, suna so a biya kudin, don karbo ‘ya’yansu, amma dai idan aka biya kudin, don sakin su, to za su sake dawowa domin sake daukar wasu yaran”.
Bukarti ya ce biyan kudin fansa ka iya zama barazana ga gwamnati domin ‘yan bindigar za su yi amfani da kudin fansar ne domin kara wa kansu karfi.
”Idan aka ba su kudi, karin makamai suke saya, da karin kayan aiki, su kuma sake zuwa su saci wasu daliban da suka fi wadannan yaran yawa”.
Masanin ya ce bincikensa ya nuna masa cewa gwamnatin Buhari da ta gabata ta biya mayakan Boko-Haram kudin fansa kimain yuro miliyan uku, wajen sakin daliban makarantar Chibok, kimanin 120.
”Amma ta’addancin da Boko-Haram suka yi bayan biyan su kudin fansar, ya fi ta’addancin da suka yi kafin a biya su kudin fansar”, in ji masanin.
Ya ce a lokacin mayakan kungiyar sun samu karin karfi, inda suka sayo kayan aiki mai yawan gaske.
”A lokacin mun samu labarin cewa Boko-Haram ta aika a sayo mata motoci kirar Hilux kimanin 50, suka samu karin makamai da sauransu”, in ji Bukarti.
Don haka nee masanin ya ce biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga ba mafita ba ne.
Ya kuma yi misali da abin da ke faruwa yanzu haka a kasar Haiti, inda ‘yan bindiga suka ce idan firaministan kasar bai sauka ba, kasar ba za ta zauna lafiya ba, kuma saboda karfin da suka yi dole ne firaminsitan ya sauka.
”Sannan kuma ka duba abin da ya faru kwanakin baya a Ecuador inda ‘yan bindiga suka yi wa dan takarar shugaban kasa gargadi kan magana da yake yi a kansu, suna masu cewa idan bai daina ba, zai dandana kudarsa, da ya sake magana a kansu suka je har gidansa suka harbe shi har lahira”.
”Ga kuma Mexico inda ‘yan bindiga ke zuwa har kurkuku su fasa, domin fitar da shugabannin gungun masu safarar kwaya idan an kama su”, in ji Bukarti.
Ya ce matukar Najeriya ta ci gaba da biyan ‘yan bindiga kudin fansa, to akwai fargabar cewa za a je irin matakin da wadancan kasashen suke ciki.
Wace hanya ya kamata gwamnati ta bi?
Barista Bukarti ya ce idan gwamnati ta ce ba za ta biya kudin fansa ba, to kuwa wajibi ne a gare ta ta samo hanyar da za ta bi don kubutar da daliban.
”Tun da gwamnati ta ce ba za ta biya ‘yan bindiga kudin fansa ba, to kuwa ba nade hannu za ta yi ta zauna ba, a jira ‘yan bindigar su dawo da yaran da kansu ba, ba kuma za a kirawo su don a roke su su mayar da yaran ba”, in ji shi.
Masanin tsaron ya ce a ganinsa mafita kwai ita ce gwamnati ta tura gungun dakarun tsaron kasa da na sama zuwa cikin dazukan da ake tunanin an tafi da daliban, domin ceto su.
”Abin da ya faru shi ne bayan sace daliban, gwamnatin tarayya ta tura sojojin sama, amma matsalar ita ce ‘yan bindigar nan sun koyi yadda za su boye wa jirgin sama, don haka ta jirgin sama kadai ba za a iya ceto daliban nan ba”, in ji shi.
Barista Bukarti ya ce hanya daya da za a iya ceto daliban ita ce a tura sojojin kasa da motocinsu, da kayan aikinsu, sannan a tura jiragen sama wadanda su kuma za su rika aika wa sojojin kasa bayanai kan abubuwan da suke gani a dajin, don samun sauki gudanar da aikin ceton.
”Maganar yara ake yi kimanin 300, don haka ba allura ba ce, ballantana a ce za ta shige cikin kasa ta bace, ba mutum daya ko biyu ba ne balle a ce ba a gansu a dajin ba, yara ne kimanin 300 ban da ma su ‘yan bindigar kansu”.
Ya ci gaba da cewa su kansu ‘yan bindigar da suka sace daliban a yanzu a gajiye suke wato barci ya dame su saboda aikin tsaron yaran nan da suke yi.
”Abincin da za su ci ma yana neman gagarar su, su kansu yaran suna cikin mawuyacin hali saboda yanayin da suke ciki a daji”, in ji Barista Bukarti.
Masanin ya ce hanya daya da za a bi don kubutar da wadannan yara ita ce amfani da sojojin kasa.
”Abin da ya sa nake jaddada maka sojojin kasa, a baya sojojin sama ake turawa, kuma dazukan nan ba wata kasa ba ce kasarmu ce, kuma ‘yan bindigar nan ba su kai sojojin Najeriya komai ba, kyale su ake yi shi ya sa suke cin karensu babu babbaka”, in ji shi.
Ko amfani da karfin soji zai yi illa ga daliban?
A duk lokacin da aka yi maganar amfani dakarfin soji don kubutar da mutanen da ‘yan bindiga ke sacewa, abin da ke fara zuwa zukatan mutane shi ne watakila hakan zai iya yin barazana ga lafiya ko ma ran mutanen da ‘yan bindigar suka sace.
To sai dai Barista Bukarti ya ce ‘yan bindigar da suka sace daliban ba su da kayan aikin da za su iya yin yaki da sojojin Najeriya.
”Baya ga rashin kayan aiki, ‘yan bindigar yanzu a gajiye suke, ga yunwa ga galabaita, kuma ba su da kayan yakin da za su iya yin gaba da gaba da sojojin Najeriya”.
Me zai samu yaran idan aka bar su a hannun ‘yan bindiga?
Barista Bukarti ya ce ”a baya mun ga yara ‘yan mata da ‘yan bingidar suka sace, inda suka yi musu auren dole, auren haramun, suka rikayi musu fyade, har suka rika yi musu ciki suka haifi ‘ya’ya da wadannan ‘yan bindigar”.
Ya ce a ganin iyaye da yawa da a bar ‘ya’yansu cikin wannan hali, sun gwammace a yi yaki don ceto yaran da Allah ya ceta, wadanda kuma Allah ya yi za su mutu, su mutu.
”Kuma ga wadanda suka mutun hankali zai kwanta cewa ba wani dan iska ba ne ya je ya yi musu fyade ya wulakanta su ya kashe su ba”.
”Abin da nake tabbatar maka shi ne idan dai aka tura sojojin kasa da isasun kayan aiki, ga sojojin sama suna tsorata su ta sama suna kuma tura wa sojojin kasa bayanai, wallahi mutanen nan ba su da karfin da za su iya yakar sojojin Najeriya, lokaci daya za a murkushe su tare da kwato yaran
‘Yan bindigar ba za su kashe yaran ba’
Barista Bukarti ya ce idan sojojin Najeriya suka tunkari ‘yan bindigar ba za su iya kashe yaran ba, saboda tsoro zai shiga ransu, sannan kuma da yawa suna ganin idan suka dinga harbe-harbe da makaman nasu karewa za su yi .
”Ka da ka yi mamaki ma idan aka tunkare su, su zubar da yaran nan su gudu, saboda a baya mun ga idan aka takura musu, suke sakin wadanda suka kama, don su tsira da rayuwarsu”.
Bukarti ya ce tun da gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta biya kudin fansa ba, to bai kamata ta zauna ta nade hannunta, ta jira dawowar yaran ba.
Don haka dole ne a tunkare su da sojojin sama da na kasa.
Masanin tsaron ya ce abin da ya kamata shagaban Najeriya Bola Tinubu ya yi, shi ne ya bai wa shugabannin rundunonin sojin sama da na kasa umarnin cewa indai ba a ceto yaran nan ba, to ka da wanda ya koma Abuja a cikinsu, domin kuwa ba su da amfani alhalin yaranmu suna cikin daji.
Daliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga
Chibok:Â A shekarar 2014 mayakan Boko-Haram sun sace daliban makarantar sakandiren ‘yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno.
Sai bayan shekaru da sace daliban mayakan sun sako wasu daga cikin daliban a wani yunkuri na shiga tsakani da kungiyoyi masu zaman kansu suka yi.
To sai dai har yanzu akwai gomman daliban makarantar Chibok da ke hannun mayakan Boko Haram da har yanzu ba su dawo gida ba, duk da cewa a lokuta daban-daban a kan samu dalibai daya, biyu da ke kubuta daga hannun mayakan kungiyar a wasu lokuta ma da ‘ya’yan da suka haifa da mayakan.
FUG Gusau:Â Haka ma Barista Bukarti ya ce har yanzu akwai sauran daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau da wasu ‘yan bindiga suka sace cikin shekarar da ta gabata.
Leah Sharibu:Â Tana cikin gomman daliban makarantar sakandiren Dapchi a jihar Yobe da mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2018, kodayake mayakan sun saki sauran daliban, amma har yanzu suna ci gaba da rike wata daliba mai suna Leah Sharibu saboda ta ki ficewa daga addininta na kirista.
Dutsin Ma:Â Haka ma har yanzu akwai sauran daliban Jami’ar Dutsin Ma a jihar Katsina da ‘yan bindiga suka sace a watan Oktoban shekarar da ta gabata da har yanzu ba a sako su ba.
Ya dace a yi amfani da masu shiga tsakani?
A baya a wasu lokuta a kan yi amfani da masu shiga tsakanin domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su a kasar, shin ko hakan zai sake yin aiki a nan?
Barista Bukarti ya ce duk inda aka yi amfani da mai shiga tsakani to wani abu aka biya, don sakin wadanda aka yi garkuwar da su.
”Ko dai a biya kudi, ko a yi yarjejeniyar sakin wasu fursunonin ‘yan bindigar da ke tsare a hannun gwamnati”.
Mataimakin shugaban hukumar kwashe Shara ta Kano ya kama Aiki
Gwamnati na ƙoƙarin ƙara yawan jami’an tsaro a Najeriya – Sanata Ƴar’adua
Ya kuma ce duk abin da aka yi daga cikin biyun nan kara jefa kasa cikin bala’i aka yi.
”Misali yuro miliyan uku da aka biya wajen ceto ‘yan matan Chibok, ai wannan ma kungiyoyi masu zaman kansu ne ciki har da Red Cross suka shiga, haka ma a ceto ma’aikatan NNPC da malaman jami’ar Maiduguri su ma irin wannan yarjejeniya aka yi daga ciki har da sako wasu mayakansu da ke kurkuku”, in ji shi.
Ya kuma ce daga baya an ga yadda mayakan da aka saka suka koma dai suka ci gaba da kaddamar da hare-hare.
Barista Bukarti ya ce inda batun masu shiga tsakani za a yi, to fa dole ne a biya kudin fansa, ko a saki mayakansu da ke tsare a hannun gwamnati,
”Kuma wannan ba zai zama mafita ba kan wannan matsala, domin kuwa za su sake karfi ne su zo su aikata wani harin da ya fi wannan ma”.
Barista Bukarti ya ce ya kamata gwamnati ta dauki matakin gaggawa wajen ceto yaran, tun suna tare wuri guda, kafin daga baya a rasa inda yaran suke.
BBCH