Wani Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Ya Shaidawa Yan Sanda Cewa, Tsoron Kar Ya Mutu Ne Ya Sanya Shi Tserewa Daga Dajin Zamfara Zuwa Kano.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta Kama wani matashi mai suna, Ibrahim Sani , da ake kira da ( Giwa) Mazaunin garin Wake dake Karamar hukumar Birnin Magaji ta jahar Zamfara.

Tun a Ranar 24 ga watan Yuni 2024, da misalin karfe 2:25pm na Rana , Jami’an rundunar yaki da Masu garkuwa da mutane reshen jahar Kano, ne Suka samu nasarar Kama matashin.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa, Ibrahim Giwa, Ana zargin yana daya daga cikin yan bindigar da Suka addabi jahar Zamfara da makotan jahohi, wajen yin garkuwa da mutane da kuma hallaka mutane da dama.

Cikin Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumar sa da aikata wa.

Wanda ake zargin ya shaida jaridar idongari.ng, cewa hukumomin Tsaro a jahar Zamfara sun addabe su , ta hanyar kashe su, shi yasa ya gudo zuwa jahar Kano, don tsira da rayuwarsa.

” sace-sacen da muke Yi muna tarar da garuruwa muna kashe yan banga suna suna kashe mu, sannan mu na korar shanun jama’a cewar ” Ibrahim Sani ( Giwa)”.

Ya Kara da cewa sojoji da Jami’an yan sanda ne , Suka hana su sakat, a dazukan da suke aikata laifukan ta’addanci.

” na Yi shekara biyu Ina yin garkuwa da mutane, kuma akalla na kashe mutane 20 a cewar Ibrahim Giwa”.

Rundunar Yan Sandan jahar Kano ta Kara da cewa yanzu haka Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *