Wani dan kasuwa a Kano ya zargi wasu yan sanda da yunkurin karbar Nagoro a wajen sa

Spread the love

Wani dan Kasuwa a jahar Kano, ya zargi wasu jami’an yan sanda biyu da yunkurin karbar na goro a hannunsa bayan ya siyo kayan da yake siyarwa.

Dan kasuwar mai suna Mutawakkil Rabi’u, ya yi zargin cewa, Jami’an yan sandan 2 sun tare shi bayan ya siyo kayan Kwalliyar mata ( Custimetics) a kasuwar Sabongari Kano da yammacin ranar Lahadi.

Mutawalkil, ya ce yan sanda sun shaida masa cewar wai babu Namba a jikin wani mai Glycerine, don haka sun kama shi.

Sakin Murja Kunya daga gidan yari ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta

Legas za ta hana amfani da robar tekawe daga gobe Litinin

Dan kasuwar ya karabda cewa, ya nuna mu su risitan kayan siyayyar amma suka ki amince wa, har suka nemi sai ya basu kudi inda suka ya ce sai dai suka shi ofishinsu.

Bayan anje ofishin yan sanda na kasuwar Sabongari, ne aka barshi ya tafi da kayansa, bayan wasu sun yi magana.

Dan kasuwar ya yi zargin cewar yin hakan murkushe kasuwanci ne a jahar Kano, a dinga kama kayan da ba na laifi ba ko kuma wadanda aka haramta shigowa da su.

A karshe ya yi kira ga mahukunta da su , dauki tsautsauran mataki ga dukkan wanda aka samu da laifin yunkurin karbar rashawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *