Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Kumbotso Kano, ta dage ci gaba da sauraran shari’ar da Alhaji Sa’id Dogo Me mai , ya yi karar wani yaronsa mai suna Halifa Garba , bisa zargin bata masa suna da kuma zagi.
Tunda farko mai karar ya shigar da orafinsa, a wajen jami’an yan sandan shiya ta daya wato zone one Kano, inda su kuma suka gurfanar da matashin a gaban kotun.
Mai gabatar da kara Insifekta Salisu Abdullahi, ya karanto masa kunshin tuhume-tuhumen da ake yi masa inda nan ta ke ya amsa laifin yin zagi amma ya musanta zargin bata suna.
- Jerin sunayen jakadu da aka yada na karya ne – Gwamnatin Najeriya
- Yan Sandan Kano Sun Tabbatar Da Rasuwar Mutane 2 Sanadiyar Fadan Daba.
Bayan Kotun ta kafa masa shaidun jin ikirari, lauyan dake kare wanda ake zargin Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya roki kotun da ta sanya shi, a hannun beli , amma mai gabatar da karar ya yi suka kan rokon inda ya shaidawa kotun cewar tunda ya amsa lifinsa na farko a yanke masa hukunci domin bayar da shi beli zai kawo cikas ga shari’ar.
Mai shari’a Mansur Ibrahim Bello, ya umarci ma su gabatar da kara su kawo shaidunsu kan tuhuma ta 2 da ake yi matashin , inda ya bayar da umarnin tsare shi a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 16 ga watan Disamba 2024.
Lauyan wanda ake tuhumar Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya ce basu gamsu ba da yadda salon shari’ar ke tafiya, don ba a basu damar da ta kamata ba, tun daga wajen jami’an yan sandan zone one, kan rashin karbar dukkan bayanansu duk da cewar suna da hujja ta hanyar hotuna da murya da kuma hoto mai motsi.
Barista Badamasi Gandu, ya kara da cewa iyayen wanda ake karar ne suka zargi mai karar da yunkurin bata wa dansu tarbiya, ta hanyar turo masa da hotuna, bidiyo harda murya bisa wata bukata da sabawa koyarwar addinin musulinci.