Yan sanda sun cafke magidancin da ya yi yunkurin hallaka matarsa dan ya kara jari

Spread the love

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta cafke wani dan kasuwa kan yunkurin kashe matarsa don ya samu damar sayar da talabijin dinsu ya kara jari a shagonsa a Jihar Bauchi.

Magidancin mai shekaru 35 ya shiga hannu ne bayan ya yi amfani da tabarya wajen dukan matar tasa da nufin hallaka ta.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Buchi SP Mohammed Ahmed Wakil, ya ce an garzaya da matar Asibitin Kwararru na Bauchi domin kulawar da ita a sakamakon raunukan da mijin ya yi mata da tabaryar.

Ya kara da cewa tuni kwamishinan yan sandan jahar CP Auwal Musa ya bayar da umarnin fadada bincike a sashin manyan laifuka da jahar , kuma da zarar an kamala za a gurdanar da shi a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *