Kano: Wani mtukin Adaidaita sahu ya mayar wa da fasinjan sa wayoyin hannu Iphone 12 promax guda 3 da aka manta.

Spread the love

 

Wani matashi dake sana’ar tuka Baburin Adaidai sahu mai suna Abduljabbar Umar Sharada Kano, ya mayar da wasu wayoyi guda uku kirar Iphone 12 pro max, da aka manta, wadanda kimarsu ta kai naira miliyan daya da dubu dari shida da hamsin.

Daya daga cikin ma su sana’ar saida wayoyin a kasuwar Farm Center Kano, ne ya manta wayoyin a baburin din, daga kasuwar wayoyin zuwa kasuwar Kantin Kwari.

Matukin baburin Adaidai sahun, Abduljabbar Sharada, ya shaida wa jaridar Idongari.ng , ta wayar tarho cewa, lokacin da aka manta wayoyin Magriba ta yi, kuma ya tashi daga aiki domin ya wancin yan kasuwar wayoyin sun rufe shagunan su.

Ya kara da cewa, hakan ne ya sanya shi ya bari sai washegari , ya nemi wani dan unguwarsu, da yake kasuwar wayoyin domin taimakama masa wajen yin cikiyar ma su wayoyin.

” Ina fada masa sai ya ce ai yasan shagon domin akwai addreshin su da Logon shagon”

Wata kotu a Kano ta umarci yan kasuwar magani ta Sabongari su tashi su koma Dangoro

Hukumar Hisbah a Kano ta cafke Ramlat Princess bayan ta tallata kanta a fanfen bidiyo cewar duk namijin da zai aure ta sai ya kawo macen da za su yi latata.

Abduljabbar Sharada ya ce bayan sun hadu da mai wayoyin, ya yi farin ciki sosai domin ya mayar da hakkin da ba na nasa ba.

Mamallakin wayoyin mai suna , Anas Uzo, ya yaba wa matashin bisa gaskiyar da ya nuna.

Anas Uzo, ya yi kira ga sauran matuka baburan Adaidaita sahu, su yi koyi da Abduljabbar Sharada, idan an manta kaya ko wani abu su dinga mayar wa da ma su su.

Lokacin da mai wayar zai bayar da kudin ga matashin

A Karshe mallakin wayoyin ya ba wa , mai sana’ar Adaidaita sahun naira dubu hamsin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *