Wani mutum ya yi yunƙurin kashe kansa a Masallacin Ka’aba

Spread the love

Jami’an tsaro na musamman da ke kula da Masallacin Harami da ke birnin Makkah sun fara gudanar da bincike kan mutum da ya yi yunkurin halaka kansa, inda ya hau bene na sama na Masallacin domin ya faɗo ƙasa.

An garzaya da mutumin zuwa asibiti domin samun kulawar da ta dace, sai dai ba a bayyana ƙasar da ya fito ba.

Rundunar ta musamman mai kula da tsaron masallacin Harami ta bayyana a shafinta na X cewa “an kammala binciken da ya kamata,” amma babu wani ƙarin bayani kan lamarin.

A shekarar 2018, wani mahajjaci mai shekaru 26 ya kashe kansa a Masallacin Harami, lamarin da ya haifar da firgici da fargaba a tsakanin alhazai da masu ibada a Masallacin.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Makkah ya bayyana a watan Yunin 2018 cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike kan wa


ni lamari, inda wani mahajjaci ya yi tsalle daga kan wani rufi a unguwar Mas’a ya kuma faɗo ƙasa, abin da ya yi sanadiyyar rasa ransa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *