Wani rikici da aka danganta da kabilanci wanda ya barke tsakanin kauyukan Gululu da ‘Yan-Kunama a jihar Jigawa, ya yi sanadin mutuwar mutum aƙalla tara.
Rikicin ya samo asali ne sakamakon zargin da aka yi wa wasu matasan Fulani da ɓalle wani shagon kayan masarufi, inda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki.
Sai dai zuwa yanzu, an samu nasarar shawo kan rikicin wanda kuma ya janyo asarar gidaje da dama.
- Kungiyoyin Masu Bukata Ta Musamman JONAPWD Sun Nesanta Kansu Da Shirya Zanga-zangar Matsa Lamba Ga Gwamnatin Kano
- NDLEA Ta Kama Wata Mata Da Yayanta 2 Da Zargin Safara Da Siyar Da Kayan Maye A Kano
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ta Jigawa, DSP Lawan Shi’isu Adam, ya shaida wa BBC cewa tuni aka aika jami’an tsaro karkashin jagorancin kwamishinan ƴan sandan jihar zuwa yankin domin kwantar da hankali.
“Za mu gudanar da bincike don ganin an kama waɗanda suka aikata wannan laifi da kuma hukunta su,” in ji DSP Lawan.
Ya ce hankali ya fara kwanciya a garuruwan kuma jami’an tsaro suna ta kai kawo don tabbatar da cewa ba a sake samun tashin hankali ba.