Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 13, Karkashin jagorancin mai shari’a , Zuwaira Yusuf Ali, ta sanya ranar 1 ga watan Maris 2024 domin fara Sauraran karar da wani mai suna Sagiru Kiyashi Madobi, (Sojan Baka), ya shigar da gidan Radiyon Arewa da Rabi’atu Abdullahi da jami’an Yan sanda da sauran mutane 9 don kotun ta dakatar da kama shi.
Ana dai zargin Sagiru Sojan Baka, da laifin yin Sojan Gona da sunan ma’aikacin Arewa Radio Kano, harda karbar wasu kudade daga hannun wata mata da sunan zai nema mata tallafi da sunan shi Dan jarida ne.
Bayan bullar wadannan al’amura ne Arewa Radio ta yi korafinsa a Ofishin ‘Yan sandan Madobi domin a kama shi, hakan ya sanya shi garzaya gaban Kotun don ta dakatar da su daga yunkurin kama shi.
Lauyan dake kare Arewa Radio da Rabi’atu Abdullahi, Barr Umar Isah Sulaiman ya bayyana cewa, Sagirun yana shigo wa gidan Radiyon a matsayin sojan baka, har ya samu damar yin bidiyo da hotuna a jikin alamar tambarin Arewa radio , kuma yake sanya su a shafin facebook.
“a nanne wata Rabi’a ta ga hotunan sa, suka ci gaba da bayanai sai ya nemi wasu kudade a wurin ta cewar zai nema mata tallafi na wani mara lafiya da ta ke da shi, inda yake ta karbar kudade a POS, kuma yana cewa shi dan jarida ne da kuma amfani da sunan Arewa radio” Lauyan Arewa Radio”.
Ya kara da cewa daga baya ne suka gano, sojan gona yake yi mu su, inda gidan radiyon ya shigar da korafi a wajen yan sandan saboda gudun bata suna.
Barista Nura B Abdullahi shi ne Lauyan mai kara ya ce Wanda yake karewa na da damar ya garzaya gaban Kotun yana kan doron doka.
” doka ce ta bayar da dama mutum yana zargin cewa za a tauye masa hakkinsa , to ya garzaya kotu don ta hana su” Lauyan wanda ake zargi”.
Jaridar Idongari.ng ta ruwaito cewa Kotun ta daga zaman shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Maris 2024 domin sammacin ya riski sauran wadanda Sagir ya yi kara a gaban kotun.