Wani Mutum Ya Fadi Kasa Bayan Ya Zubawa Kansa Shinkafar Bera A Abincin A Kano

Spread the love

Wani mutum ya zubawa abincinsa shinkafar Bera, akan Titin Audu Bako Way Dake Jihar Kano.

Ana Zargin mutumin ya zuba gubar ce bayan ya sayi Wata shinkafa da miya kuma Sai da ya fara ci sannan ya nunawa mutane abunda ya zuba cikin abincin.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, ya shiga gidan abinci ne ya siyo sannan ya zuba gubar kafin ya ci.

Yanzu haka an garzaya da shi zuwa Asbitin Nassarawa don bashi kulawar gaggawa sakamakon faduwa da ya yi kuma baya cikin haiyacinsa.

Zuwa yanzu dai ba a San dalilin sa na aikata Hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *