Wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne sun harbe wani ɗan Sarkin Hausawa har lahira a Benin, babban birnin jihar Edo.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗan mai suna Danladi, an kashe shi ne a shagon abokinsa mai nisan kilomita 100 da ofishin ƴansanda na Esigie da ke ƙaramar hukumar Oredo na jihar ta Edo.
Wani shaida wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce Danladi na zaune ne a shagon abokinsa lokacin da ƴan ƙungiyar asirin suka isa a cikin wata mota ƙirar jeep GLK Benz tare da harbinsa har sau biyu.
Ya ce, “Danladi mutumin kirki ne. Shi ne Sarkin Hausawan yankin, mutuwarsa ta janyo gagarumar giɓi a iyalansa da kuma matar da yake shirin aura,” in ji shi.
An ruwaito cewa matashin yana shirin ɗaura aure da amaryarsa a wata mai zuwa kafin afkuwar lamarin.