Wasu Gidajen Mai Sun Fara Cinikin Dare Maimaikon Na Ido Na Ganin Ido A Kano.

Spread the love

Rahotanni na cewa , wasu daga cikin gidajen da ake siyar man Fetur sun Fara cinikin dare maimakon na Rana, da aka Saba gani.

Cikin daren Jiya Talata jaridar idongari. ng, ta ruwaito cewa, ana siyar da man kan farashin da bai wuce naira 730 ba , a gidajen man yan kasuwa.

Yayinda gidan NNPC ke siyarwa kan naira 620 kowacce Lita daya, amma akwai dogwayen layukan ababen hawa.

Tun daga misalin karfe 12:00am na Daren jiya Talata , jaridar idongari. ng, ta fara kewaya wasu daga cikin gidajen man a sassan kwaryar birnin Kano, inda ta gano cewar akwai man amma ba Kowa ne yake siyarwa da Rana ba , sai daddare ga yan bunburutu.

Sai dai gidajen mai da dama ba siyarwa da Rana.

Akwai dai gidajen mai kalilan da suke siyar da man da Rana , amma ba su da yawa, inda daddare kasuwar yan bunburutu ke ci, wadanda suke zuwa da manyan jarkoki don siyan man.

Al’umma dai na kokawa kan yadda mafi yawan gidajen man suka garkame ba tare da bayar da man ba, domin KO a Ranar Talata, jaridar idongari.ng, ta ga wani gidan mai da aka kawo man amma suka ki siyarwa da al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *