Mazauna Garin Hausawar Danamliki unguwar Kwari , a Karamar hukumar Kumbotso Kano, sun Yi kira ga mahukunta da Su kawo mu su dauki, don Gina mu su Katanga a makabartar yankin , sakamakon yadda ake zargin batagarin mutane na shiga cikin makabartar suna binne wasu abubuwa a Kaburbura.
Bukatar hakan ta biyo bayan hangar wata Mata sanye da likabi, wadda ake zargin ta shiga makabartar yankin sannan ta binne Kwan Kaji guda uku ma su rubutu tare da Wata takadda ita ma mai dauke da rubuce-rubuce a cikin Kabari kamar yadda Idongari.ng, ta ruwaito.
Al’ummar yankin sun zargi Matar da yin sihiri na Neman duniya ko neman mallakar miji.
- Zargin Badakala: Babbar Kotun Jahar Kano Ta Hana Lauyoyi Yin Magana Da Yan Jarida A Karar Da Gwamnatin Jahar Ta Shigar Da Ganduje Da Wa su Mutane 6
- Kotun Ƙolin Najeriya ta ce gwamnoni su daina riƙe kuɗin ƙananan hukumomi
Daya daga cikin matan unguwar gidan kwarin, ta shaida wa idongari.ng, cewar ta na cikin gida aka shaida Mata faruwar lamarin, kuma lokacin da Matar da ake zargi da shiga makabartar sai da ta faki idon mutane Kafin ta shiga, don kawai fitowar ta aka gani da cikin makabartar sanye da Likabi.
Wani matashi dake yankin ya Kara da cewa Matar duniyar kawai ta ke nema, domin lokacin da ta fito ta na sanye da Lakabi da kuma Face Mask a fuskarta, wadda ba lallalle ba ne a iya gane ta.
Yanzu haka dai sun ce ba wannan ne farau ba , da aka Saba binne mu Su abubuwan sihiri a cikin makabartar , amma a cewar Su an Yi na karshe domin duk Wanda Suka Kama zai dandana kudarsa.
Tuni dai aka tono takaddar da kuma kwailwayen guda uku, wadanda matasan yankin Suka kudiri aniyar soyasu Su cinye Su.
A karshe sun yi fatan mahukunta za su taimaka mu su wajen gine makabartar.