Masu garkuwa sun sace fasinjojin bas kan hanyar Abuja

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya a cikin wata motar safa guda biyu da ke kan hayarsu ta zuwa Inele-Eteke Ogugu, a yankin Kogi ta gabas.

Tuni rudunar yansandan jihar ta Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Williams Ayah ya fitar ta ce baturen ‘yansandan yankin da jami’an tsaro na sa kai, da wasu mafarauta na chan suna fafutukar ganin sun ceto wadan da aka yi garkuwar da su.

Kotu Ta Sa Ranar Sauraren Rokon Daukaka Kara Kan Hukuncin Kisan Abduljabbar

Kotu Ta Sa Ranar Sauraren Rokon Daukaka Kara Kan Hukuncin Kisan Abduljabbar

Ya ce lamarin ya rutsa da motar safa mallakin kamfanin GIG mai cin fasinjoji 12 da wata kirar Sienna mallakin kamfanin sufuri mallakin kamfanin ABC da ke dauke da mutun biyu a ciki. Sai dai daga bisani jami’an tsaron sun ceto direban motar kamfanin na GIG, a cewar mai magana da yawun rudunar ‘yansandan.

A cewar sa kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kogi Bethrand Onuoha ya umarci ruduna ta musamman na tactical squad, da ‘yansandan kwantar da tarzoma, da na yaki da taddanci da sauran sassan ‘yansanda na musamman, don ganin an ceto sauran wadan ake zargin an yi garkuwar da su, cikin koshin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *