Wasu Yan Daudu Sun Yi Wa Ofishin Hisbah Rotse Tare Da Kwantar Da Tutocinsu A Unguwar Bachirawa Kano.

Spread the love

Wasu matasa da ake zargin Yan Daudu ne sun Yi wa ofishin hukumar Hisbah na yankin Bachirawa Kano, Rotse inda suka farfasa gilasan motarsu, da yukurin kone ofishin da kuma tsugunar da Tutocin ofishin hukumar.

Rahotannin da jaridar Idongari.ng, ta samu sun bayyana cewa, tunda fari Yan kwamitin Unguwar ne suka fito aikin sintiri, sakamakon Barayin da suka addabe Su da yawan sace-sace , sai suka ci Karo wasu Matasan su uku kuma bayan sun hangi Yan kwamitin tsaron Unguwar suka fara gudu.

Sai dai Yan kwamitin Unguwar sun bi su abaya , har suka ga sun shiga cikin wani lungu tare fadawa wani gida inda jami’an hisbar suka bukaci lallai sai yan Daudun sun fito.

Mu na Nema wa Gwamna Abba kabir Yusuf Afuwa daga Wajen Mal Ibrahim Aminu Daurawa-Rabiu Kiru.

Murja Ta Kai Ƙarar Hisbah Gaban Kotu

Guda daga cikin Mambobin kwamitin tsaron Unguwar Habibu Abubakar , ya bayyana cewar, Yan Unguwar sun fito cikin daren domin ganin wadanda ake zargin, kuma suna bude kofar aka ga Matasa sama da 10 a cikin daya.

Inda wasu suke shaye-shaye, wasu kuma sun shafa bilitin a fuskarsu .

Ya kara da cewa sakamakon haniya ta Yi Yawa makota sun fito, har suka shawarce Su cewar abar lamarin zuwa Safiya , wadanda suka amince da hakan.

Bayan gari ya waye ne aka garzaya ofishin hukumar Hisbah domin gana wa , da dan Daudun mai suna Nakabara, amma yaki zuwa ofishin hukumar Hisbah.

Ana dai zargin Nakabara da tattara wasu Yan Daudu kusan mutum 40, har suka jiya wa jami’an Hisbah ciwo da farfasa Gilasan motarsu da yunkurin kone ofishin bayan sun yi barana.

Rahotanni na cewa jami’an hukumar Hisbar na ci gaba da yaki da aiyukan Badala a sassan jahar.

Daya daga cikin Yan Daudun ya zargi Yan Kungiyar da dauke masa Wata jakar Kudi , mai dauke da Dalolin Amurika da ya karbo a birnin tarayya Abuja, inda kungiyar ta musanta zargin da cewar kalen sharri ne kawai don bata mu Su suna, kuma kudin dake cikin jakar bai Kai. Naira dubu biyar ba, kuma an bashi kudinsa.

Yanzu haka dai an shigar da maganar a shelkwatar rundunar Yan sandan jahar Kano don fadada bincike Kan lamarin.

Wannan dai ba zai rasa nasaba da kalaman gwamnan jahar Kano ba, Engr. Abba Kabir Yusuf, Kan aiyukan da hukumar Hisbah ke yi , inda ya ce akwai kurakurai wajen aiwatar wa.

Kuma bayan fitar kalaman na sa Babban kwamandan hukumar ta Hisbah Shiek Mallam Aminu Ibrahim Daurawa ya Yi murabusa daga Kan kujerar da aka Nada shi.

Ana dai zargin kalaman kalaman gwamnan Kano, me ya karawa wadanda ake zargi da aikata Badala karfi har Suka samu damar yin Rotse a ofishin hukumar Hisbah.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *