Wani tsagin yayan jam’iyar NNPP, a Minna babban birnin jahar Naija, wadanda suke adawa da jagorancin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sun gudanar da taron kone Jajayen Huluna a jahar.
Shugaban masu adawa da madugun kwankwasiyar Dr. Gilbert Agbo, ne ya jagoranci mutanen a sakatariyar jam’iyar, inda ya ce dakatarwar da aka yi wa Kwankwaso daga jam’iyar a jahar Lagos, ya nuna cewa shi, ba dan jam’iyar ba ne yanzu haka.
Dr. Gilbert , wanda ya sanya idanu kan yadda aka kone Jajayen Hulunan, ya bayyana cewa tsagin kwankwasiyar wani bangren ne na raba kan yayan jam’iyarsu don haka ba za su lamunci wannan lamari ba.
- An tsinci gawar ƙaramin yaro a ƙarƙashin gada
- An kama wani mutum da bindiga a wajen yaƙin neman zaɓen Trump