Wata babbar Kotu ta hana ci gaba da sauraren karar da aka shigar da mawaki Rarara bisa zargin sukar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari

Spread the love

Wata babbar Kotu a Jihar Nasarawa, ta dakatar da Kotun Majistire mai namba 1 , ci gaba da sauraren karar da wani matashi mai suna Sani Ahmad Zangina ya shigar da fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara, bisa zarginsa da sukar tsohon Shugaban kasa Muhammad Buhari.

Lauyan da ke jagorantar tawagar lauyoyin Rarara, Barrister A. I Ma’aji, ya bayyana wa manema labarai cewar sun daukaka kara a gaban Mai Shari’a Abdullahi H. Shamsu Shama na Babbar Kotun dake Doma tun watan da ya gabata, bisa rashin gamsuwa da umarnin Kotun Majistiren na  tilasta wa Rarara ya bayyana a gabanta.

 

Sai dai lauyan wanda ya shigar da karar, Barista Isah Hassan Nalaraba, ya ce ba su da masaniyar daukaka karar da lauyoyin mawakin suka yi, abin da kawai ya sani shi ne, akwai zaman kotun a ranar juma’a.

Idan ba a manta ba idongari.ng, ya ruwaito muku cewa Kotun Majistiren  dake Lafia ta sanya, 2 ga watan Fabrairun 2024 a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraren karar.

Abun jira again shi ne yadda shari’ar za ta ci kaya a gobe juma’a kamar yadda kotun majistiren ta sanya a baya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *