Wata babbar kotu a jihar Jigawa ta yanke wa wasu ma’aurata hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin kashe wata mata mai suna Salamatu.
Kotun ta ce ta same su da laifin kashe matar mai kimanin shekara 30, wadda suka zarga da mutuwar ɗansu sanadiyyar maita.
Da yake yanke hukunci, mai sharia’a Ado Yusuf Birnin-Kudu, ya ce kotun ta same su da laifin aikata kisan, don haka ne ta yanke musu wannan hukunci.
“Don haka wannan kotu ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari saboda laifin haɗa baki don aikata laifi da kuma kisa ta hanyar rataya saboda aikata kisan kai,” in ji Ado.
An dai fara zaman sauraron shari’ar tun shekara ta 2019, inda masu gabatar da ƙara suka gabatar da shaidu biyar da kuma rahoton bincike na lafiya.
Kotun ta ce ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, inda haka ne ma ya sa ta yanke wa ma’auratan da wasu ƴan uwansu biyu wannan hukunci.
Yanzu dai suna da damar ɗaukaka ƙara cikin kwanaki 90.