Wata babbar kotun jahar Kano ta ci gaba da sauraren shari’ar wasu yan sanda da aka dakatar daga aiki kan zargin fashi da makami

Spread the love

Babbar kotun jahar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Faruk Lawan , ta ci gaba da sauraren tuhumar da ake yi wa wasu jami’an yan sanda wadanda aka dakatar daga aiki, saboda zargin su da yin amfani da kakinsu wajen kokarin kwace kudaden wasu yan kasuwa a jahar.

Wadanda ake tuhumar sun hada da, Ali Abdullahi (Zaki) , Abdulkadir Ibrahim, Yusuf Buba, Yusuf Sabo , Rabi’u Umar da kuma Muntari Kabiru.

Ana dai zarginsu da hada kai dan aikata laifi da kuma aikata fashi da makami.

Tun a baya dai wadanda ake zargin sun musanta kunshin tuhumar da ake yi mu su da cewar ba su aikata laifin ba.

Lauyar gwamnatin jahar Kano Barista A’isha Salisu ta bayyana wa kotun cewar a shirye suke su gabatar sa shaidun su.

Mai shari’a justice Faruk Lawan, ya sanya ranar 27 da 28 ga watan Janairun  2024 , dan fara gabatar da shaidun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *