Wata babbar kotun jahar Kano ta fara sauraren shaidu kan kisan matar da aka zarga da maita

Spread the love

Babbar kotun jahar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Usman Na’abba, ta fara sauraren shaidu kan tuhumar da ake yi wasu mutane da laifin kisan kan wata mata mai suna Dahare, wadda suka zarga da maita.

Lamarin dai ya faru ne tun a shekarar 2023, a kauyen Dadin Kowa dake karamar Wudil Kano.

Ana zargin daya daga cikin wadanda ake tuhuma mai suna Rabiya Ibrahim ce ta shaida wa, Daluta Ibrahim, Abdulaziz Yahaya, Faisal Yahaya, Ibrahim Abdu da kuma Ayuba Abdurraham, cewar ta yi mafarki Dahare Maiyace.

karan ta wannan labarin Hukumar hisbah ta jahar Kano ta ce za ta ci gaba da kama ma su yada badala a Tiktok

karan ta wannan labarin Ba ni da masaniyar biyan masu sa ido a zaɓe $6m da Emefiele ya yi

Lauyan gwamnatin jahar Kano Barista Lamido Abba Sorondinki, ya gabatar da shaidu guda uku ciki harda yayan marigayiyar , kuma sun yi rantsuwar za su bada shaidar gaskiya.

Lauyan dake kare wadanda ake tuhuma barista Shazali Ashiru, ya roki kotun ta bayar da belin wadanda yake kare wa.

Mai shari’a Usman Na’abba, ya sanya ranar litinin 19 ga watan Fabarairun 2023 domin yin nazari kan rokon beli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *