Wata babbar kotun jahar Kano ta tsare wanda da ake zargin da caccakawa Kamalu Sadik wuka a cikinsa

Spread the love

Gwamnatin jahar Kano ta gurfanr da wani matashi mai suna Musbahu Ya’u, a gaban babbar kotun jahar Knao mai namba 14 da ke zaman ta, a unguwar Miller Road bisa zarginsa da cakawa wani mai suna Kamalu Sadik , Wuka a cikinsa har sai da hanji ya fito, sakamakon wata sa’insa da ta shiga tsakaninsu.

Bayan gurfanar da shi , a gaban kotun lauyan gwamnatin jahar Kano , Barista Lamido Abba Sorondinki , ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa , inda nan ta ke ya musan ta zargin.

Mai gabatar da karar ya roki kotun ta ba su wata ranar domin gabatar da shaidun su.

Lauyan wanda ake zargi Barista Ahmad Ali, bai yi suka ba kan rokon lauyan gwamnatin , sai dai ya yi rokon cewar kotun ta ba da umarni, a ba su takaddun da za a gabatar a gaban ta.
Kotun ta aike da wanda ake tuhumar zuwa gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 28 ga watan Fabarairun 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *