Babbar kotun jahar Kano, mai lamba 13, karkashin jagorancin justice Zuwaira Yusuf, ta ce zata sanar da ranar yanke hukunci kan shari’ar nan da ake zargin wasu mutane 7 da satar yara a jahar.
Wannan na zuwa ne bayan da kotun ta kammala karbar bayanan bangarorin shari’ar na karshe.
A bangaren Lauyar gwamnatin jahar Kano, Barista Khadija Aliyu Umar, ta kammala gabatar da jawabinta na karshe, inda itama lauyar wadanda ake zargin Barista Hasiya Mohd Imam, ta rufe jawabin ta na karshe kan shari’ar.
Wadanda ake zargin sun hada da , Poul Owne, Mercy poul, Egbere Ogiba, Emmanuel Igwe, Loutis Duru, Monica Oracha da kuma Chenelo Efediagwe.
Tun a shekarar 2019 ne jami’an yan sandan jahar Kano, suka samu nasarar kama mutanen da ake zargin da satar yara, inda bincike ya kai ga gano yara 9 a jahar Anambra dake kudancin Nigeria kamar yadda www.idongari.ng, ta ruwaito.
A baya dai wata babbar kotun jahar Kano ta samu Poul, da laifuka 38, da suka jibanci satar yara a Kano, inda kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 104, a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya , Alkaliyar Kotun justice Zuwaira Yusuf, ta bayyana cewa za ta sanar da ranar yanke hukunci, kan tuhumar da ake yi mutanen da aka gurfanar.
- Kano State Government Urged To Save Kano Pillars Teams From Relegation
- Yadda ‘ya’yanmu huɗu suka kuɓuta daga masu garkuwa – Chefsafmar