Wata babbar kotun jahar Kano, ta sanya ranar 27 ga watan Nuwamba 2024, don sauraren dukkanin rokon da aka shigar da babban bankin Nigeria ( CBN) da kuma hukumar raba arzikin kasa, da dai sauransu don hana su rike kudaden kananan hukumomin Kano.
Shugaban gamayyar kungiyoyin ma’aikatan kananan hukumomin na kasa, NULGE, Ibrahim Muhd, Ibrahim Uba Shehu, Ibrahim Shehu Abubakar, Usman Isa, Sarki Alhaji Kurawa da Malam Usman Imam, ta bakin lauyansu Barista Bashir Yusuf, sun shigar da karar a ranar 1 ga watan Nuwamba, don neman kotu ta hana wadanda ake kara su rike kason kananan hukumomin jahar Kano.
A zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan ma su , Barista Bashir Yusuf Muhammad, ya shaida wa kotun cewar a shirye suke su ci gaba da shari’ar.
Sai dai ya ce wanda ake kara na 46 CBN, ya ba su takaddar martani a ranar Laraba, inda su kuma suka yi gaggawar ba su amsar martanin saboda shari’a ce da shafi miliyoyin mutanen jahar Kano.
Lauyan CBN, ya Yi suka da cewa kotun Bata da hurumin sauraren Shari’ar.
Har ila yau, Lauyan CBN da Lauyan UBA da Bankin Keystone, Ganiyu Ajape da Emanuel Awuaikyejh, sun shaida wa kotun cewa ba su shirya ba, inda suka roki kotun ta ba su wata rana.
Alkalin kotun, Mai shari’a Ibrahim Musa Muhammad, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba, domin sauraren duk rokon da ke gaban kotun.
- CP SALMAN DOGO GARBA PAYS VISIT TO COALITION OF ULAMA, QADIRIYYA, TIJJANIYYA LEADERS
- Na yi farin cikin kama Simon Ekpa – CG Musa