Babbar kotun jahar Kano, Mai namba 11, karkashin jagorancin Mai Justice Nasir Saminu , ta sallami wata Dattijuwa Mai suna A’isha Hashim, mazauniyar Garin Dakasoye dake karamar hukumar Bebeji, bisa Zarginta da kashe wata wata karamar Yarinya Mai shekaru 2 da kuma jefa gawarta a Rijiya.
Tun a ranar 22 ga watan Augustan 2022, aka Zargi Dattijuwar da kashe Yarinyar Mai suna Maryam, Inda jami’an Yan Sanda suka kama ta don gudanar da bincike, daga bisani kuma suka Gurfanar da ita a gaban kotu.
Lauyan Gwamnatin jahar Kano, Barista Zaharaddin Mustapha, ya gabatar da shaidunsu, ya yin da wadda Ake Zargin ta kare kanta.
Alkalin kotun justice Nasir Saminu, ya ce shaidun da aka gabatar ba su tsaya ba, don haka ya wanke Dattijuwar daga Zargin.
Lauyan Dattijuwar , ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin kotun, har ya tabbatar da cewar daman shaidun da lauyoyin Gwamnatin suka gabatar , su da kansu sun ce, ba Ido da Ido suka ga Dattijuwar ba.
Anata bangaren wadda kotun ta sallama ta ce kotun ta Yi mata adalci domin a lokacin da lamarin ya Faru ta na Gona.