Wata Babbar Kotun Tarayya A Kano Ta Bayar Da Belin Mai Kamfanin Anadariya Traveling Agency.

Spread the love

Babbar kotun tarayya mai lamba 3 dake zaman ta a jahar kano, ta bayar da belin, Hajiya Rabi Lawan mai kamfanin Anadariya Traveling Agency bisa sharuddai guda 6 kamar yadda alkalin kotun Mai shari’a Simon Amobeda ya gindaya.

Sharadi na farko, shi ne a kawo mutane 2 wadanda za su tsaya mata akan N20m kowannen su, sharadi na biyu kuma su kasance yan uwanta ne na jini, sharadi na uku, su bayyana shaidar mallakar gida ko fili mai dauke da shaidar mallaka ta gwamnati C.of.O. sharadi na hudu, za su bayar da takardun shaidar biyan kudaden haraji ga gwamnatin tarayya na tsawon shekaru 3, sharadi na bitar, Rabi zata ajiye dukkannin takardun shaidar fita kasashen ketare da passport dinta, a karshe Rabi Lawan zata dinga zuwa kotu duk zaman da za’ayi, idan kuma ta karya daya daga cikin wadannan sharuddai kotun zata karya belin ta data bayar.

 

Tunda fari dai, Wasu mutane daga sassa daban daban a jihar kano da wasu jihohin suka kulla alakar kai mutane kasashen ketare domin yin aikin kamfani da aikace aikace, mutanen sun shigar da karar ne domin neman hakkin su a wajen Hajiya Rabi Lawan, har Zunzurutun Kudi sama da Naira Miliyan dari 2.

Tun a baya, an karantowa Rabi kunshin tuhumar da ake yi mata, amma ta musanta, saidai lauyan Rabi Lawan, Barr Abdullahi Alhassan Usman ya Nemi a bayar da belin ta.

A zaman kotun na ranar Talata, kotu ta yi kwarya kwaryar hukunci inda ta bayar da belin ta, sannan kotun ta sanya ranar 23 ga watan janairu na shekarar 2025 domin cigaba da Shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *