Jihar Assam da ke arewacin Indiya ta haramta cin naman shanu a bainar jama’a, ciki har da wuraren sayar da abinci da kuma taruka.
Wannan ɗai ƙari ne kan wata doka da ta takaita sayar da naman na shanu a kusa da wuraren bauta, kamar yadda babban minista Himanta Biswa Sarma ya bayyana ranar Laraba.
Sai dai, duk da haka za a iya sayan naman daga kantuna a kuma iya cinsa a gidaje ko hukumomi masu zaman kansu a jihar.
Cin naman sa dai wani abu ne zai iya tayar da hargitsi a Indiya, kasancewar ana girmama shanu musamman ma ƴan addinin Hindu, waɗanda suka kai kashi 80 na yawan al’ummar ƙasar.
Jihohi da dama da jam’iyyar Firaminista Narendra Modi ta BJP ke mulka -wadda ke da iko a jihar ta Assam – sun saka tsauraran dokoki kan yanka shanu a shekarun baya-bayan nan.
Kusan kashi biyu bisa uku na jihohin Indiya 28, yawancin waɗanda jam’iyyar BJP ke mulka, sun haramta yanka shanu da cin naman sa baki-ɗaya ko kuma a wasu wurare.
Ana dai zargin ƙungiyoyin bijilanti masu kula da shanu da tirsasa haramcin ta hanyar tayar da rikici, abin da a wasu lokuta ke janyo munanan hare-hare kan Musulmi masu sayar da naman shanu da kuma kasuwancin dabbobu.