Wata kotu ta aike da wani Aljani zuwa gidan gyaran hali a Kano

Spread the love


Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Danbare Kano, ta aike da wani mutum zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya bisa zargin sa da aikata laifin Tsoratarwa da kuma Damfara , wanda yin hakan ya saba da sashi 227 da 208 na dokokin shari’ar shekarar 2000.

An gurfanar da Yazid Abdullahi, a ranar juma’ar da ta gabata, inda ake zargin ya kira wata mata mai suna Hajiya Binta Aminu Gwazaye, a wayar salula har ya shaida mata cewar shi Aljani ne , dan haka ta bashi nira dubu arba’in da biyar idan kuma bata bayar ba zata ga abunda zai faru da ita.

Gwamnatin Najeriya ta gargaɗin NLC kan zanga-zangar da ta shirya yi a ƙasar

Gwamnati za ta yi maganin masu yi wa kasuwar chanji zagon-ƙasa’

Bayan ya tsoratar da ita ne, Hajiya Binta Gwazaye, ta shigar da korafi a ofishin yan sanda, wadanda su kuma suka cafke shi.
Bayan gurfanar da shi a gaban kotun mai gabatar da kara Inspecter Bashir Wada, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa, inda nan ta ke ya amsa laifinsa.
Sai saboda kuracewar lokaci mai shari’a Munzali idris Gwadabe, ya aike da shi zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa nan da mako biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *