Babbar kotun jahar Kano, mai lamba 13 ta bayar da belin matarnan mai suna, Shamsiyya Ashiru, wadda ake zargi da kashe dan kishiyarta, mai suna Naziru Ashiru dan kwanaki 18 a duniya.
Tun a shekarar 2022, ake zargin matar da kisan yaron ta hanyar bashi guba, a garin Lamba dake karamar hukumar bichi Kano.
Mai shari’a Justice Zuwaira Yusuf, ta bayyana cewa lauyan wadda ake zargin ya gamsar da kotu kan rashin halatar ma su gabatar da kara, don haka kotun ta bayar da belin ta, bisa sharadin kawo mutane biyu sannan kuma sai dan sandan kotu yaga gidajensu kuma za su ajiye naira dubu dari a gaban kotu.
Kotun ta sanya ranar 4 ga watan Fabarairun 2025 don ci gaban shari’ar.
- Wata Babbar Kotun Kano Ta Ce Zata Sanar Da Ranar Yanke Hukunci Kan Sauran Mutanen Da Ake Zargi Da Satar Yara.
- Kano State Government Urged To Save Kano Pillars Teams From Relegation