Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Rijiyar Lemo Kano, ta bayar da umarnin tsare wani mutum a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya, sakamakon zargin da ake Yi masa na dukan Dan kishiyar Yayarsa da Bulala.
Tunda fari jami’an Yan Sanda ne suka Gurfanar da Wanda Ake Zargin bisa kunshin tuhumar samar da rauni.
- CP Salman Dogo Ya Gana Da Jamiāan Yan Sanda Don Fadada Sintiri Da Tabbatar Da Tsaro A Kano
- Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta PCACC Ta Tsare Dan Uwan Kwankwaso, Shugaban Karamar Hukuma Kan Zargin Badakalar Kwangilar Siyan Magani A Kano
Mutumin da ake Zargin mai suna Abdullahi Nafi’u , ya musanta kunshin tuhumar da ake Yi masa.
Ana Zargin ya yi amfani da wata Bulala, ya zane Aliyu Abdullahi har yaji masa ciwo saboda Yana Zargin mahaifiyarsa sun Samu sabani da Yayarsa wadda suke kishiya da kishiya .
Alkalin kotun Mai shari’a Malam Umar Sunusi Danbaba , ya aike da shi zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 25 ga watan Satumba 2024.