Kotun shari’ar addinin musulinci dake Unguwar Gama Kano, bisa jagorancin mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ta aike wani matshi mai suna Musa Okashatu Gobirawa, zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya bisa zarginsa da laifin Razanarwa, wanda yin hakan ya saba wa sashi na 227 na kundin shari’ar Penal Code 2,000.
An gurfanar da shi ne sakamakon korafin da wasu mutane da suka hada da Muhammad Sani Hussain da Bashir Namoriki ne suka shigar , kuma suna cikin yan kwamitin Unguwar Gobirawa, sakamakon barazana da ya yi mu su cewar sai ya hallaka su.
Wannan lamari ya samo asali ne , a matsayin su na shugabannin yankin suka gabatar da taro, har suka tattauna muhimman abubuwa, sai kawai ya zo a fusace tare da yin ikirin sai yaga bayansu.
Bisa wadannan kalaman ne , Dattawan Unguwar da yan kwamitin suka shigar da korafinsu a wajen yan sandan Bachirawa, daganan suka tura shi zuwa sashin binciken manyan laifuka sakamon ikirarin kisan kai da ya furta zai yi.
Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja
Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala
Bayan gurfanar da shi a gaban kotun, mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala , ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa , kuma ya amsa da cewar tabbas ya fada, bisa dalilin cewar yan kwamitin ne suka fusata shi kan wani fili da gyara amma za su kwace masa.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed , ya aike da shi zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 11 ga watan Janairu 2023.
IDONGARI.NG